Mayakan Boko Haram 443 da suka tuba sun mika wuya a Borno

0
106

A kalla kimanin tubabbun ’yan ta’addan Boko Haram 443 da iyalansu ne suka mika wuya ga rundunar sojojin Najeriya a Jihar Borno.

Rahotanni na nuna cewar matakin ya biyo bayan tserewar da suka yi ne daga wani kazamin harin da kungiyar ’yan ta’adda ta ISWAP ta kai a kan su a mako guda da ya wuce a jihar Borno.

A yayin harin dai, a cewar Zagazola Makama, wani kwararre a fannin yaki da tada kayar baya a yankin Tafkin Chadi, fadan harin ya kai adadin wadanda suka mutu zuwa 300 a tsakanin kungiyoyin ta’addancin biyu.

A cewarsa, ’yan ta’addan na Boko Haram 223 da iyalansu ne suka mika wuya ga dakarun MNJTF tsakanin ranar 7 zuwa 10 ga watan Maris, 2023 a Diffa da Gueskerou da ke Jumhuriyar Nijar.

Bayan haka, ya kara da cewa, “’Yan Boko Haram 220 sun kuma mika wuya ga sojojin Operation Hadin Kai (OPHK) a ranar 10 ga watan Maris, 2023.

“’Yan ta’addar sun yi ikirarin cewa fafatawa tsakanin bangarorin biyu ya tilasta musu tserewa zuwa wurare masu aminci.”

Tun a ranar 27 ga Fabrairu 2023, Boko Haram ke ta tserewa daga yankunansu, a sakamakon munanan hare-haren da aka kai wa kungiyoyin a Gaizuwa, a yankin Mantari-Gabchari-Kashimiri-Maimusari na karamar hukumar Bama.

Zagazola Makama ya kuma ce sauran maboyar ’yan Boko Haram din sun hada da na yankin Yale a Kananan Hukumomin Konduga da Magumeri na Jihar.

Ya kara da cewa, gwamnatin Nijar ta hannun hukumar yada labarai da hulda da jama’a ta ce: “A wannan makon ne ‘yan ta’addan suka gudanar gagarumar gudun hijirar da iyalan ta hanyar kaura daga dajin Sambisa zuwa yankin Tafkin Chadi mai iyaka da Jamhuriyar Nijar.

Daraktan Ayyukan Yada Labarai na tsaro na hedikwatar tsaron Najeriya, Manjo-Janar Musa Danmadami, ya bayyana cewa ’yan ta’adda 1,332 tare da iyalansu ne suka mika wuya a cikin makonni biyun da suka gabata ga rundunar soji.

Ya alakanta karuwar mika wuya ga yadda ake ci gaba da samu da gwabza kazamin fada tsakanin kungiyar Boko Haram da takwararta ta ISWAP.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here