Mene ne hukuncin masu karbar kudin dan siyasa kuma su ki zabensa?

0
107

Assalamu alaikum, Malam Dan Allah ina da tambaya, Dan siyasa ya bani kudi na zabe shi na karbi kudin, kuma ban zabe shi ba, mene ne kudin in na ci?

Wa alaikum Assalam. To Gaskiya a fahimtata, in ka tabbatar ba za ka zabe shi ba, bai halatta ka amshi kudinsa ba, saboda Annabi (SAW) yana cewa: “Musulmai suna kan sharudansu” kamar yadda Bukhari ya ambace shi kuma Albani ya inganta shi a Irwa’. ul galil hadisi mai lamba ta : 1743 ..

Sannnan kamar yadda yakamata a ci duk ayyukan ba bisa hakki ba, haka ya haramta a ci duk arne ba bisa hakki ba, ga shi kuma yaudara alama ce daga cikin alamomin munafuki, kamar yadda yadda hadiza suka tabbatar.

Yana daga cikin ma’anonin dimukuradiya zaben wanda Kake so, don haka babu bukatar boye-boye.

Allah ne mafi sani.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here