Mijina ba ya son haihuwa, ko ya halatta na hana shi kaina? (Fatawa)

0
102

Assalamu alaikum. Malam ina da matsala tsakanina da mijina, ba ya son haihuwa ko saduwa muka yi sai dai ya zubar a waje, ga shi kuma yarinyar mu daya, ita ma bai damu da ita ba, ina da laifi In na hana shi kaina?

Wa alaikum assalam. To ‘yar’uwa yana da kyau ki sani cewa ya halatta a samu tazara a tsakanin iyali, abin da musulunci ya hana shi ne kin haihuwa kwata-kwata, saboda babbar manufar aure shi ne hayayyafa, don a samu wadanda za su bauta wa Allah.

Zubar da maniyyi a wajan Farji ya halatta saboda hadisin Jabir wanda yake cewa “Mun kasance muna yin azalo (zubar da maniyyi a waje yayin saduwa) a lokacin da Kur’ani yake sauka, kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 4911.

Hadisin da ya gabata yana nuna cewa: Bai halatta mace ta hana mijinta kanta ba saboda hujjar yana AZALO, tun da Alkur’ani bai haramta ba.

Saduwa rukuni ne babba a aure, Wannan yasa Annabi (SAW) ya ce: “Mace ta amsa kiran mijinta ko da tana kan kaskon tuya ya kira ta, sannan la’ana ta tabbata ga wacce mijinta ya yi fushi da ita, saboda ya neme ta ba ta ba shi hadin-kai ba Kula da abin da mutum ya haifa wajibi ne, ciyar da su kuma sadaka ne, wannan ya sa za ki dinga yi wa mijinki nasiha cikin ladabi don ya fahimci gaskiya.
Allah ne mafi sani.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here