Wani jirgin ruwan fasinja dauke da mutane ya nutse

0
89
Baraguzan jirgin da ya nutse a gabar tekun Gabon a ranar Alhamis din da ta gabata, ya kashe akalla mutane uku bisa ga wani rahoto na wucin gadi, kuma ana ci gaba da neman wasu 34 da suka bace, in ji Firaminista a yau lahadi.

Akalla yaro daya ya mutu, da kuma manya guda biyu, lokacin da Esther Miracle, jirgin dakon kaya da jigilar fasinjoji da ke da alaka da Libreville da tashar mai na Port-Gentil, ya nutse da tsakar daren alhamis.

Har yanzu adadin wadanda suka mutu kwanaki uku da rabi bayan afkuwar lamarin, na nuni cewa mutane uku ne suka mutu, 34 kuma sun bace.

Gwamnati ta tabbatar da adadin mutane 161 da suka hada da fasinjoji da ma’aikatan jirgin, wadanda suka tashi da yammacin Laraba daga Libreville.

Ba mu dakatar da binciken ba,” in ji Firaminista Alain-Claude Bilie-By-Nze da tsakar rana a wata ziyarar da ya kai ga iyalan wadanda a tashar talabijin ta Gabon Première.

Ya kara da cewa “A yayin da muke magana, wani jirgin ruwa dauke da masu ruwa da tsaki na kokarin gano tarkacen jirgin, ba za mu dakatar da binciken ba har sai mun gano tarkacen jirgin kuma mun tabbatar mun dauko dukkan gawarwakin.” Ya zuwa yanzu dai an ceto mutane 124 da ransu.

Dangane da wata jita-jita a shafukan sada zumunta kimanin mutane biyar da aka gano a daya daga cikin tsibiran Sao Tome and Principe, mai tazarar kilomita sama da 300 daga wurin da jirgin ya nutse, “mun tuntubi hukumomin Sao Tome, tare da Interpol da sojojin ruwa na ‘yan kasuwa, sai dai basu gamsu ba da amshoshi da suka samu daga wadanan mutane, “in ji shugaban gwamnatin.

A ranar Alhamis, mai shigar da kara na Libreville, André Patrick Roponat, ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa, nan da nan aka lkaddamar da wani bincike na laifuka don kokarin gano musabbabin nutsewar jirgin: ko dai lalacewa ko kuma kuskure ,wanda a halin da ake ciki “mai shi zai amsa tambayoyi daga masu bincike.

Jirgin wanda na kamfani mai zaman kansa, Royal Cost Marine (RCM), galibin wadanda suka tsira da ransu na sanye da rigunan kare rai daga cikin mutane da dama da kamfanin dillancin labarai na AFP ya gani sun isa birnin Libreville a safiyar ranar Alhamis.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here