Wani saurayi mai shekara 22 mai sana’ar dinki da ke zaune a jihar Adamawa, mai suna Muhammed Bala, ya shiga hannun ‘yan sanda saboda kashe wanda suke neman budurwa daya da shi.
Muhammed yana zaune a garin Mararaba da ke karamar hukumar Madagali, ya kashe makocinsa wanda suke neman budurwa daya da shi mai suna Bakura,sakamakon fadan da ya kaure a tsakaninsu saboda budurwa.
Muhammed ya yi sanadiyyar mutuwar Bakura sakamakon rikicin da ya barke tsakaninsu kan wata budurwa mai suna Maryam Mohammed.
Muhammed ya tabbatar da cewa, ya daba wa Bakura wuka a wuya, saboda yana neman budurwarsa wadda ya ce, ta yi alkawarin za ta aure shi,kuma tun tsawon shekara uku suke tare.
Kamar yadda ‘yansanda suka ce,Bakura da kansa ya tabbatar da cewa, budurwar ta ce yarinyar ta ce Muhammed ya daina zuwa wajenta.
Rikici ya kaure lokacin da suka hadu a gurin yarinyar, inda nan take fada ya kaure a tsakaninsu wanda nan take Muhammed ya zaro wuka ya daba wa Bakura ya fadi ya mutu.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar Adamawa SP Suleiman Nguroje, ya tabbatar da faruwar wanan lamarin kuma ya ce, wanda ake zargin yana hannu, za kuma su kai shi kotu da zarar sun gama bincike.