’Yan bindiga sun sace mutum 9 a Abuja

0
102

’Yan bindiga sun sace mutum tara a rukunin gidaje na Grow Homes da ke Kuchibayi a Kubwa, yankin Babban Birnin Tarayya Abuja.

Maharan dai wadanda yawansu ya kai kusan 20, rahotanni sun ce sun yi wa wajen kawanya ne wajen misalin karfe 11:30 na daren Juma’a.

Wani mazaunin yankin da ya ce sunansa Hassan ya ce an kwashe mutanen ne daga cikin gidaje biyu.

Ya kuma ce lamarin ya jefa mazauna yankin cikin fargaba.

A cewarsa, “Jiya [Juma’a], wajen misalin karfe 11:30 na dare, wasu gungun ’yan bindiga sun kai hari kan rukunin gidaje na Grow Homes da ke kan hanyar Kuchibayi.

“A yayin harin, mun rika jin karar harbe-harben bindiga kuma fargaba ta kama kowa.

“Yau da safe mun je rukunin gidajen, inda muka iske yawan maharan sun kai wajen 20, kuma sun rika bi gida-gida ne suna yi wa mazauna ciki kwace.

“Sun kuma sace kusan mutum tara daga gida biyu, cikinsu har da mata da kananan yara.

“Sun bi ta wani dajin da ya hada wajen da kauyen Paze. Tun safe ’yan sanda da masu gadin rukunin gidajen suka shiga dajin don ganin ko za su iya ceto mutanen,” in ji Hassan.

Da aka tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Abuja, SP Josephine Adeh, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce yanzu haka sun bazama kokarin ceto wadanda aka sace daga cikin daji.

Ta ce jim kadan da samun rahoton kai harin ne jami’ansu suka yi wa wajen dirar mikiya, lamarin da ya sa suka gudu cikin daji da mutum taran.

Josephine ta shawarci mazauna yankin da kada su tsorata, a madadin haka su taimaka wa jami’an ’yan sanda da ingantattun bayanan da za su taimaka wajen kama bata-garin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here