DA DUMI-DUMI: CBN ya ba wa bankuna umarnin ci gaba da hada-hadar tsofaffin takardun kudi — Soludo

0
251

Gwamnan jihar Anambra, Charles Soludo ya sanar cewa babban bankin Najeriya CBN ya ba da umarnin bankuna su ci gaba da hada-hada da tsofaffin takardun Naira.

Da wannan ne Soludi ya umarci mazauna jiharsa da su ci gaba da amfani da tsofaffin takardun naira 200 da 500 da 1,000 tare da sababbin takardun kudin a ko’ina cikin jihar.

Cikin wata sanarwa ta musamman da Charles Soludo – wanda tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya ne – ya fitar, ya ce CBN ya umarci bankunan kasuwanci a kasar da su ci gaba da biyan abokanan huldarsu da tsofaffin takardun kudi.

Sannan kuma su ci gaba da karbar tsofaffin takardun kudin a duk lokacin da aka gabatar da su.

Gwamnan jihar Anambra ya ce ya tabbatar da sahihancin umarnin yayin wata hira da ya yi da Gwamnan Babban Bankin, Godwin Emefiele ta wayar tarho a ranar Lahadi da daddare.

Soludo ya ce Gwamnan CBN ya bayar da wannan umarnin ne yayin wani taro da Babban Bankin ya yi da bankunan kasar da aka yi a ranar Lahadi 12 ga watan Maris.

Gwamnan na Anambra ya kuma bukaci al’ummar jihar da su kai karar dukkan bankin da ya ki bin umarnin babban bankin na biya da karbar tsofaffin takardun kudin.

Yana gargadin cewa gwamnatinsa za ta rufe duk bankin da ya bijire wa wannan umarnin.

Kokarin da Aminiya ta yi na tabbatar da hakan daga mahukunta ya ci tura, inda an gaza jin ta bakin mai magana da yawun Babban Bankin, Isa Abdulmumin.

Sai dai wasu majiyoyo sun shaida wa wakilinmu cewa, an yi taruka daban-daban daga nesa tsakanin Emefiele da Shugabannin Bankunan Kasuwanci a Yammacin ranar Lahadi, wanda hakan ke nuna alamar kamshin gaskiya a lamarin.

Har ya zuwa kawo wannan rahoto, Babban Bankin dai bai musanta ikirarin da Gwamna Soludo ya yi ba.

Ana iya tuna cewa, a ranar 3 ga watan Maris ne Kotun Koli ta yanke hukuncin ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kudin har zuwa 31 ga watan Disamban 2023.

Wasu gwamnatocin jihohin kasar ne dai suka shigar da kara a gaban kotun, suna neman a dage wa’adin da CBN ya sanya na daina amfani tsofaffin kudin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here