Akalla mata 24 ke takarar neman kujerar gwamna a sassan Najeriya yayin zaben jihohi 28 da zai gudana a karshen makon nan, alkaluman da ke nuna karuwar mata a harkokin siyasar kasar ta yammacin Afrika.
Wannan ne karon farko da ake ganin tururuwar mata don neman madafun iko a sassan kasar musamman daga yankin Arewaci, inda wasu alkaluman hukumar zaben Najeriyar INEC ke nuna cewa, mata 2 ne kadai suka samu tikitin tsayawa takara karkashin manyan jam’iyyun kasar 3 da suka kunshi APC mai mulki da PDP da kuma jam’iyyar LP cikin jam’iyyun da ke shirin fafatawa a zaben na ranar 18 ga watan nan.
Fitacciyya cikin wadannan ‘yan takara mata akwai Aishatu Dahiru ta jam’iyyar APC a jihar Adamawa da ke neman kujerar gwamna, sai ‘yan takara mata 2 da ke neman kujerar ta gwamna a jihar Abia da suka kunshi Gladys Johnson-Ogbuneke ta SDP da kuma Lancaster Okoro ta jam’iyyar PRP.
Can a jihar Akwa Ibom ma akwai mata biyu da ke fafatawa don neman kujerar gwamnan jihar da suka kunshi Ekanem Abasiekeme ta jam’iyyar AA da kuma Udoh Emem Monday ta SDP.
Sauran ‘yan takarar Mata sun kunshi Roseline Chenge ta jam’iyyar ADP a jihar Benue kana Abubakar Fatima ta ADP a jihar Borno sai Ibiang Marikana da ke neman kujerar Gwamna a Cross River karkashin jam’iyyar ADP.
Jihar Delta ma na da ‘yan takarar Gwamna 2 da suka kunshi Onokiti Helen Agboola ta jam’iyyar Accord kana Cosmas Annabel ta APP, yayinda can a jihar Ebonyi Chinenye Igwe ke takarar Gwamna karkashin jam’iyyar APM sannan Ogochukwu Nweze ta Jamiyyar SDP a Enugu.
A jihar Jigawa ta arewacin Najeriya Umar Binta Yahaya ce ke yi wa jam’iyyar AA takarar gwamna yayin da a jihar Kano ake da ‘yan takara mata 2 da suka kunshi Yakubu Furera Ahmad daga jam’iyyar BP kana Mahmud Aisha daga jam’iyyar NRM.
A jihar Kwara akwai Motunrayo Jaiyeola karkashin jam’iyyar APM, yayin da jihar Lagos ke da mata ‘yan takarar gwamna biyu ciki har da Funmilayo Kupoliyi ta APM da Roseline Adeyemi ta APP kana Patricia Tsakpa ta ADP a jihar Nasarawa sannan Khadijah Abdullahi-Iya ta APGA a jihar Neja sannan Aduragbemi Euba ta jam’iyyar YPP da ke neman gwamna a jihar Oyo.
Sauran ‘yan takarar mata da ke neman kujerar gwamna sun kunshi Beatrice Itubo ta LP a jihar Rivers sannan Hadiza Usman ta jam’iyyar ZLP a jihar Zamfara.