Kamfanin Meta mallakin Facebook ya sake korar ma’aikata dubu 10,000

0
115

A karo na biyu, kamfanin Meta mallakin Facebook da sauran shafuka ya sake korar ma’aikata 10,000 saboda matsin tattalin arziki.

Kamfanin a ranar Talata ya ce za a rage yawan ma’aikatansa masu daukar aiki, sannan ya sake rage masu kula da na’urori a karshen watan Afrilu, sai na bangaren kasuwanci a karshen watan Mayu.

Kamfanin ya kuduri aniyar sake fasalinsa tare da dakatar da shirinsa na daukar sabbin ma’aikata 5,000, sannan ya dakatar da daukar matsakaitan ma’aikata.

Shugaban kamfanin, Mark Zuckerberg ya ce, “Wannan mataki ne mai tsauri, kuma babu yadda muka iya a kan hakan.

“Hakan na nufin yin bankwana da zakakuran ma’aikatanmu wadanda suka taimaka mana wajen samun nasararmu.” in ji shi.

Ya kuma ce akwai yiwuwar hakan ya ci gaba tsawon shekaru saboda halin tattalin arzikin da ake ciki.

Damuwa kan matsin tattalin arziki saboda raguwar kudaden shiga a Amurka ya haddasa asarar ayyuka masu yawa.

Kamfanin dai, wanda ya kashe biliyoyin Daloli wajen sake fasalinsa ta yadda zai dace da bukatunsa a nan gaba, na fama da raguwar kudade tun bayan annobar COVID-19.

Ko a watan da ya gabata, sai da ya bayyana abin da ya samu, inda ya ce ya sami koma-baya a karo na uku cikin karshen shekarar da ta gabata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here