Wata ‘yar haya ta kashe mai gidan da ta ke haya ta hanyar murde masa makarfafa

0
105

Wata ‘yar haya mai suna Ifeoma Ossai ta kashe mai gidan hayanta ta hanyar cafke masa mazakuta, wanda hakan ya yi sanadin mutuwar magidancin har lahira sabida takaddamar kudin wutar lantarki a jihar Ogun.

Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta kama Ifeoma Ossai mai shekaru 33 da haihuwa bisa zargin kashe mai gidanta mai suna Monday Surulere Oladele mai shekaru 50 bisa wata karamar takaddama.

A cewar jaridar ejesgist.ng, an kama wacce ake zargin ne bayan Olaleye Taiwo ya shigar da kara a hedikwatar ‘yan sanda ta Sango Ota.

Taiwo ya kai rahoto ga ‘yan sandan cewa dan’uwansa, Oladele, ‘yar hayar gidansa ta cafke masa mazakuta kan wata takaddama ta kudin wutar lantarki.

A cewarsa, dan uwansa ya mutu sanadin cafke masa mazakuta bayan ya fadi kasa aka garzaya da shi babban asibitin Ota.

Abimbola Oyeyemi, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan, ya bayyana a ranar Talata cewa, bayan samun rahoton, DPO na sashin Ota, Saleh Dahiru, ya jagoranci jami’an bincikensa zuwa wurin da lamarin ya faru, inda suka cafke wacce ake zargin aka tura ta sashin bincike na manyan laifuka na hukumar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here