A wani sabon harin da aka kai unguwar Langson da ke karamar hukumar Zango Kataf a jihar Kaduna, an tabbatar da mutuwar mutane akalla 10 tare da jikkata wasu da dama.
Harin wanda aka ce ya faru ne a daren ranar Talata har zuwa wayewar safiyar Laraba, an ce ya faru ne duk da dokar hana fita ta sa’o’i 24 da aka kafa bayan harin da aka kai a makon jiya da ya yi sanadin mutuwar mutane 17.
A halin da ake ciki kuma, shugabannin kungiyar ci gaban al’ummar Atyap (ACDA), wadanda suka tabbatar da harin na baya-bayan nan, sun nuna rashin amincewa da jami’an tsaron da aka tura yankin domin kare rayuka da dukiyoyinsu.
Shugaban ACDA na kasa, Mista Sam Achie, ya ce, “’Yansandan tsaro da aka tura Kudancin Kaduna ba su ba mu kariya, domin an dade ana kashe-kashe ba tare da la’akari da hakan ba, amma gwamnati ta yi shiru.
Achie, wanda ya bayyana hakan a wurin da aka kai harin a lokacin da ya kai ziyara, ya jaddada cewa shiru da gwamnatin jihar Kaduna ta yi kan ci gaba da kai hare-hare a yankin abin damuwa ne.
Don haka ya bukaci gwamnati dauki matakin kawo karshen hare-haren.
Shugaban ACDA na kasa, ya yabawa rundunar MOPOL da ke yankin Langson, wanda aka ce sun fatattaki maharan, yayin da ya yi kira ga jama’a da su ci gaba da kasancewa cikin shiri domin kare kan su da dukiyoyinsu daga azzalumai.
Ya bayyana cewa wadanda suka jikkata a harin na samun kulawa a wasu asibitocin yankin.
A nasa bangaren, shugaban karamar hukumar Zango Kataf, Mista Francis Sani, wanda shi ma ya tabbatar da faruwar harin, ya roki gwamnatin jihar da ta kara tura jami’an tsaro zuwa karamar hukumar Zango Kataf, domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a a yankin.
LEADERSHIP ta tattaro, cewar maharan sun mamaye al’ummar garin ne da misalin karfe 9 na daren ranar Talata, inda suka yi ta harbe-harbe inda suka kashe jama’a, tare da raunata wasu, tare da yin awon gaba da wani mai shago a yankin, kafin daga bisani MOPOL suka fatattake su.
Kakakin rundunar Operation Safe Haven, Laftanar Kanar I.S. Takwa, bai amsa waya ba don jin ta bakinsa.