Wani soja ya harbe abokin aikin sa a jihar Borno

0
103

Wani sojan da har yanzu ba a bayyana sunansa ba wanda ke yaki da kungiyar ta’addanci ta Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas ya harbe abokin aikinsa.

A cewar majiyoyin soji, mutanen biyu sojoji ne na Operation Desert Sanity kuma sun shiga aikin soja ne a shekarar 2020.

A cewar Sahara Reporters, sojan da aka harbe ana kiransa da suna ‘Private Diko’.

Lamarin ya faru ne a ranar Juma’ar da ta gabata a Ngoshe, karamar hukumar Gwoza ta jihar.

“Suna cikin gardama, kawai sai ya dauki bindiga ya harbe shi (Diko). Dukkaninsu suna cikin ‘yan 20NA, an tura su zuwa bataliya ta 103 da ke Enugu daga baya aka maidasu jihar Borno domin yakar ‘yan Boko Haram,” kamar yadda wata majiyar soja ta shaida wa SaharaReporters.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here