Sojin Nijar sun kashe mayakan Boko Haram 30 tare da kame wasu 960

0
105

Mahukuntan jamhuriyyar Nijar sun sanar da kisan ‘yan ta’adda 30 tare da kame mabiyansu akalla 960 galibi mata da kananan yara wadanda suka kwarara kasar daga makwabciyarta Najeriya.

Gidan talibijin din gwamnatin Nijar Tele Sahel ya ruwaito ma’aikatar tsaron kasar na sanar da kisan ‘yan ta’addan 30 lokacin da dakarun Soji suka ga kwararowar adadi mai yawa na mayaka daga Najeriya ta hanyar amfani da iyakar kogin Kamadougou Yoge da ya raba kasashen biyu.

Rahotannin sun ce mayakan ‘yan ta’addan da iyalansu mambobi ne na kungiyar Boko Haram wadanda ke gujewa hare-haren mayakan kungiyar ISWAP mai biyayya ga IS wadda ke kokarin karbe ragamar ta’addanci a kasar mafi yawan jama’a a nahiyar Afrika.

A shekarar 2016 ne, Boko Haram ta rabu gida biyu inda Abubakar shekau ya ci gaba da jagorantar tsagi guda a bangare guda Abu Mus’ab albarnawi ya jagoranci tsagin da ya koma biyayya ga IS, kuma tun daga wancan lokacin ne suka fara yakar juna.

Bayanan da ma’aikatar tsaron Nijar ta fitar t ace dakarun Sojin kasar sun dakile yunkurin mayakan na Boko Haram a kokarin kaiwa ga tafkin Chadi don kafa sansani a can wanda ya kai ga gwabzawarsu a ranar 11 ga watan nan inda kaso mai yawa suka mika wuya.

Wasu majiyoyi sun bayyana cewa galibin mayakan na Boko Haram da ISWAP ta koro daga dajin Sambisa na cikin mawuyacin hali tare da iyalansu da kaso mai yawa na kananan yara da Mata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here