Bukatar kafa gwamnatin hadin kai

0
88

A ranar 1 ga watan Maris 2023 ne Hukumar Zabe INEC ta bayyana jam’iyya mai mulki ta APC a matsayin wadanda ta lashe zaben shugaban kasa da aka yi ranar Asabar 25 ga watan Fabrairu 2023.

Tinubu, tsohon gwamnan Jihar Legas wanda ya yi wa APC takara ya samu kuri’u 8,794,726 inda ya kayar da Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar jam’iyyar PDP wanda ya samu kuri’u 6,984,520.

Wanda ya zo na uku a zaben shi ne Peter Obi na jam’iyyar LP mai kuri’a 6,101,533 sai kuma Rabiu Musa Kwankwaso na jam’iyyar NNPP wanda ya zo na hudu da kuri’u 1,496,687.

A ranar da aka yi zaben shugaban kasa, ‘yan Nijeriya sun kuma zabi ‘yan majalisun kasa 469, da yawa a cikin su kuma wannan ne karo na farko na shigarsu majalisar.

Amma kuma zaben shugaban kasa, kamar dai yadda aka yi a shekarun baya, a wannan karon ma yana tattare ne da abubuwan da sukia shafi kabilanci da addini, musamman ma ganin dukkan manyan ‘yan takarar su uku sun fito ne daga manyan kabilun kasar nan.

 

Sannan kuma wadanda suka zo na biyu da na uku duk suna ikirarin sune suka lashe zaben, suna korafin cewa an yi magudi a yayin da ake tattara sakamakon zaben. Baya ga hukuncin kotun da ke sauraren karrarikin zabe da kuma hukuncin da kotun koli za ta iya yankewa daga baya babu wata dokar da za ta iya hana a rantsar da Bola Tinubu a matsayin shugaban Nijeriya a ranar 29 ga watan Mayu 2023.

Da zarar ya dare karagar mulki, zai shiga hidimar zabo ministoci da shugabanin ma’aikatu da za su taimaka masa wajen aiwatar da alkawurran da ya yi wa al’ummar Nijeriya a lokacin da yake yakin neman zabe, shugaban kasan zai kuma iyan tabbatar da ganin wanene zai zama shugaban majalisar dadttawa da kuma ta wakilai. A kan haka ne muke ganin yana da matukar muhimmanci a ra’ayinmu na mu jawo hankalin shugaban kasa Tinubu a kan bukatar a samar da gwamnatin da dukkan bangarorin kasa za su san ana damawa su a cikin gwamnatin da kuma shugabanin majalisar kasa. A siyasance, Tinubu ya kafa harkar siyasan ce a yankin kudu maso yammacin Nijeriya. Kuma kamar yadda ne bayyana da bakinsa, ya kuduri burin zama shugaban kasa ne a dukkan tsawon rayuwarsa. Tabbas wannan burinasa ne ya sanya ya yi watsi da jam’iyyar ACN inda ya shiga hadaka da jam’iyyar APC, jam’iyyar da ke da asali daga yankin arewacin Nijeriya.

A wannan hadakar a gwamnatin da ta gabata, a ware wasu yankuna a yayin zaben shugabanin majalisar kasa, yayin da arewa ta samu shugaban kasa da shugaban majalisar dattawa, yankin kudu maso yamma suka samu mataimaki shugaban kasa da shugaban majalisar wakilai, muna kira ga zabbaben shugaban kasa da kada ya bi wannan hanyar.

Amma daga dukkan alamu, bangaren shugaban kasa basu kammala bukuwan lashe zabe ba, amma sai gashi har an fara gwagwamaryar neman shugabancin majalisan dattawa da kuma ta Wakilai.

Duk da cewa, a boye ake kamun kafar neman shugabancin majalisun biyu, amma al’umma na ganin yadda al’amurran ke tafiya, inda ake yi wa wasu ‘yan majalisar kamun kafa da yawa na amfanin da makaman da ke a hannun su wadanda suka hada da bukatar da yankunan suke cii na neman ayyukan cigaba, zamu ga wasu irin wadannan salon kamun kafar daga masu neman shugabancin majalisar kasa a nan gaba kada.

Akwai wasu tanade-tanade a cikin kundin tsarin mulkin kasa da aka tabbatar da cewa, ba a juya wa wani bangare ko jiha baya ba a harkar gudanar da kasa.  Baya ga tabbatar da shugaban kasa ya zabi Ministoci daga dukkan jihohin tarayyar kasar nan, tsarin mulki ya fayyace yadda za a kafa gwmanatin tarayya da ma na wasu ma’aikatun  gwamnati ta yadda za a tafi tare da kowa da kowa don samar da hadin kan kasa.

Da babu wannan tanadin da Tinubu yana da damar ya zabi ‘yan asalin jiharsa ta Legas su zama ministoci maimakon ya zaba daga jihohi 36 a tarayyar Nijeriya, sai dai a wuraren da ba a samu wadanda suka cancaci rike wani mukami ba daga wata jiha. Doka ta tanadi a rarraba mukamai a tsakanin shiyoyyin siyasa shida na kasar nan don kowa ya san ana damawa da shi. Don haka a kwai bukatar a yi takatsantsan wajen ganin kowacce bangare na kasa ya samu wakilci a dukkan bangarorin gudanar da mukin kasar nan gaba daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here