An kori wasu manyan lakcarori hudu saboda laifin lalata da dalibai da sauran laifuka a Kwalejin Kimiyya da Kere-kere ta Jihar Kogi (Kogi Poly).
Hukumar gudanarwar Kogi Poly ta kori lakcarorin daga aiki ne bayan samun su da laifuka da suka hada da, “Neman yin lalata da kuma mugunta ga dalibai mata.”
Sauran sun hada da; “Rashin zuwa aiki, rashin ladabi, amfani da takardun bogi, saba doka da kuma karkatar da kudade,” kamar yadda kakakin kwalejin,Uredo Omale, ya sanar ranar Juma’a a Lakwaja.
Akwai kuma wadda aka kora saboda fashin aiki na wata shida, wadda aka umarce ta da dawo da albashin da ta karba na tsawon lokacin da ba ta zuwa aiki.
Hukumar kuma yi wa wasu lakcarori takwas karin girma daga matakin Principal Lecturer zuwa Chief Lecturers.