Zaben 2023 EFCC ta kama mutum 20, ciki har da ma’aikatan INEC kan sayen kuri’a By Usman Zunnurayn - March 18, 2023 0 90 FacebookTwitterPinterestWhatsApp Ofishin Hukumar EFCC da ke Ilorin, babban birnin jihar Kwara, ya kama mutum 20 bisa zarginsu da cinikin kuri’a. Daga cikin wadanda aka kama din, har da jami’in hukumar da kuma wakilan jam’iyyu a fadin Jihar.