An harbi ma’aikaciyar INEC

0
99

Wani dan bindiga ya harbi wata ma’aikaciyar wucin gadi ta hukumar zabe ta kasa (INEC), Miss Glory Effion Essien, a hanyarta ta zuwa karamar hukumar Bakassi don gudanar da aikinta a ranar zabe.

Baturen Zaben Jihar Kuros Riba, Farfesa Gabriel Yomeri ne ya bayyana hakan inda ya ce an kai ta asibiti tana karbar magani.

Gabriel ya bayyana rashin jin dadinsa da afkuwar lamarin, sai dai ya ce ya ji dadi da harbin bai lahanta mata lakar jikinta ba.

Rahotanni dai na nuna dan bindigar da ya harbe ta a baya lokacin da take kan hanyarta ta zuwa aiki a kwale-kwale, guda ne daga cikin masu tada kayar bayan da suka addabi yankin Bakassin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here