Kudaden da ke kewayawa tsakanin jama’a ya ragu zuwa Naira biliyan 982

0
84

Kudaden da ke kewayawa a tsakanin al’umma a Najeriya ya ragu zuwa naira billiyan 982 da digo 09 a karshen watan Fabrairu daga naira tiriliyan 3 da biliyan 29 da   yake a karshen watan Oktoban shekarar 2022, sakamakon sake fasalin kudin da babban bankin kasar ya yi.

Alkalumman da aka samu daga babban bankin kasar ya bayyaana cewa naira tiriliyan 2 da biliyan 3 ne aka karbe daga hannun jama’a zuwa karshen watan Janairu.

A watan  Oktoban shekarar 2022 ne gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emiefele ya sanar da shirin sake fasalin takardun naira 200, 500 da 1000.

Bayan haka ne ya bai wa ilahirin al’ummar kasar wa’adin watanni 3 kacal domin kai kudadensu banki a musanya musu da sabbi.

Emeifele ya koka da kalubalen da ke tattare da  tafiyar da harkokkin kudin Najeriya, inda ya ce dimbim al’ummar kasar na boye kudade a dakunansu ba tare da sun kai banki ba,  yana mai cewa kashi 80 na kudaden na hannnun jama’a.

Wannan tsari na babban bankin Najeriya ya haddasa karancin kudade a hannun al’umma, lamarin da ya jefa mutane cikin mawuyacin hali.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here