Wuraren da aka ci gaba da zaɓen gwamna a ranar Lahadi

0
92

A Najeriya hukumar zaɓen ƙasar ta ce za a gudanar da zaɓen gwamnan da na majalisar dokokin jihohi a wasu yankuna na ƙasar ranar Lahadi.

Hukumar ta ce hakan zai faru ne kasancewar ba a samu gudanar da zaɓen a irin waɗannan mazaɓu ba.

A wata sanarwa da ta fitar, hukumar zaɓe a jihar Rivers da ke kudancin ƙasar ta an ɗage zaɓen a ƙaramar hukumar Asari-Tobu da kuma gunduma ta 14 a ƙaramar hukumar Degema.

Sanarwar da hukumar INEC ta fitar ta ce ba a samu gudanar da zaɓen a waɗannan yankuna ba kasancewar masu kaɗa ƙuri’a sun turje wa ma’aikatan da aka tura.

Masu zaɓen sun ce ba za su yi zaɓe ba har sai sun ga jami’an tattara sakamako na gunduma.

A gunduma ta 14 kuwa ta ƙaramar hukumar Degema, nan ma masu zaɓe sun buƙaci ganin ma’aikatan da aka tura su bayyana takardun tattara sakamako, wanda kuma nauyi ne da ya rataya a kan jami’an tattara sakamako.

Hukumar ta ce a sanadiyyar haka ne aka gaza gudanar da zaɓuka a wannan gundumomi.

A ƙarshe sanarwar ta ce, INEC za ta gudanar da zaɓuka a waɗannan yankuna ranar Lahadi 19 ga watan Maris, 2023, bisa dogaro da sashe na 24 na dokar zaɓe ta 2022.

Haka nan a jihar Legas INEC ta ɗage zaɓen gwamna da na ƴan majalisar jiha a mazaɓu 10.

Wuraren da wannan ɗagewar ta shafa sun haɗa da rukunin gidaje na Victoria Garden City (VGC) da ke ƙaramar hukumar Eti-Osa.

Yayin da yake magana da manema labarai, kwamishinan hukumar zaɓe a jihar ta Legas, Mista Olusegun Agbaje ya ce ma’aikatan wucin gadin da ke aiki a yankin sun ƙi gudanar da aikinsu saboda ƙalubalen da suka fuskanta a zaɓen shugaban ƙasa.

“Muna da mazaɓu takwas a nan da masu zaɓe 6,024 da aka yi wa rajista kuma daga cikinsu 5,624 sun karɓi katin zaɓensu,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa lamarin ya shafi wasu mazaɓu biyu a rukunin gidajen.

“Bayan tuntuɓa, mun sami umarni daga hukumar zaɓe ta ƙasar cewa mu ɗage zaɓen zuwa gobe Lahadi da ƙarfe 8:30.” kamar yadda kwamishinan hukumar zaɓen ya shaida.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here