An sace baturen zabe akan hanyarsa ta zuwa cibiyar tattara sakamakon zabe a Zamfara

0
100

An yi garkuwa da jami’in hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC da shugaban tattara sakamakon zabe a karamar hukumar Maradun jihar Zamfara.

Maradun ta kasance mahaifar gwamna mai mulki, Bello Mohammed Matawalle wanda kuma shine dan takara a jam’iyyar APC da ke neman yin tazarce.

An sace sune akan hanyarsu ta zuwa Hedikwatar hukumar zabe inda ake tattara sakamakon zabe a garin Gusau bayan dauko sakamakon zaben karamar hukumar Maradun.

Kakakin hukumar INEC, Muktari Janyau ya tabbatar da sace jami’an, inda ya ce sun shigar da korafi ga ‘yansandan jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here