Napoli na shirin lashe Serie A karon farko cikin shekara 33

0
92

Kawo yanzu dai Napoli na bukatar maki 15 nan gaba domin ta lashe kofin babbar gasar tamaula ta Italiya a karon farko tun bayan 1990, wato shekaru 33 da suka gabata.

Napoli ta ci gaba da shirin lashe kofin Serie A na bana, bayan da ta je ta ci Torino 4-0 ranar Lahadi a wasan mako na 27.

Napoli ta fara cin kwallo minti tara da fara wasa ta hannun Victor Osimhen, sannan Khvicha Kvaratskhelia ya ci na biyu a bugun fenariti daga nan aka yi hutu.

Bayan da suka koma zagaye na biyu ne Osimhen ya kara na biyu kuma na uku a karawar, sannan Tanguy Ndombele ya ci na hudu.

Victor Osimhen, shi ne kan gaba a yawan cin kwallo a Serie A mai 21 a raga kawo yanzu, sannan mai biye da shi kuwa Lautaro Martinez ya ci wa Inter Milan 14.

Da wannan sakamakon Napoli ta ci wasa 10 a jere a fafatawa 11 a bayan nan a dukkan karawar da ta yi.

Torino ta ci kwallo a minti na 23, amma da alkalin wasa ya je ya duba a VAR sai ta fayyace cewar an taba da hannu kafin ta shiga raga, sai ya soke ta.

Ranar Lahadi Juventus ta je ta ci Inter Milan 1-0 a San Siro a dai gasar ta Serie A.

Wasan ya dauki zafi matuka inda aka bai wa dan kwallon Inter, Danilo D’Ambrosio da na Juventus, Leandro Paredes jan kati.

Bayan da aka ci Inter, kenan Lazio ta koma ta biyu a teburi, saboda ta ci abokiyar hamayyarta Roma 1-0.

An kuma kori dan kwallon Roma, Roger Ibanez, bayan da ya karbi katin gargadi guda biyu a wasan.

Mattia Zaccagni ne ya ci wa Lazio kwallon, wadda ta hada maki ukun da take bukata.

Daga baya alkalin wasan ya kara bayar da jan kati biyu bayan tashi a wasan, tun farko ’yan wasa sun kalubalanci juna da cacar baki da ta kai ya bai wa dan wasan Lazio, Adam Marusic da na Roma, Bryan Cristante jan kati.

Kungiyar Jose Mourinho ta barar da damar shiga gurbin zuwa Gasar Zakarun Turai ta Champions League, indq ta ci gaba da zama a mataki na biyar da tazarar maki daya tsakaninta da AC Milan ta hudu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here