PSV ta yanke wa magoyin bayanta hukuncin dakatarwar shekaru 40

0
82

PSV Eindhoven ta dakatar da wani mai goyon bayanta daga shiga filin wasanta da tsawon shekaru 40, bayan samunsa da laifin kai hari kan golan Sevilla Marko Dmitrovic yayin karawar da kungiyoyin suka yi a gasar cin kofin Europa.

Baya ga haramcin shiga filin na tsawon shekaru 40, an kuma yanke wa matashin mai shekaru 20, hukuncin daurin wata uku a gidan yari. Kafin matakin kuma dama yana karkashin haramcin shiga babban filin wasa na kasar  Netherlands.

Wani karin batu da ya dauki hankali kuma shi ne matakin dakatar da fitinannen magoyin bayan na PSV daga halartar yankin da ke kusa da filin wasa na kungiyar da tsawon shekaru biyu.

Zalika kulob din ya ce zai yi kokarin tatsar diyya daga matashin domin mika ta ga golan kungiyar Sevilla, wanda ya yi sa’a bai samu rauni ba, sakamakon kokarin kare kansa da yayi.

Bincike ya nuna cewar mai kutsen da ya faki ido ya ruga cikin fili tare da kaiwa mai tsaron ragar Sevilla hari, ya shiga kallon wasan na Europa ne, ta hanyar amfani da tikitin da abokinsa ya saya, duk da cewar yana karkashin haramcin shiga babban filin wasa na Netherlands har zuwa shekarar 2026.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here