Zababben Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida, ya sha alwashin riko da akalar jagoranci kamar yadda ubangidansa, Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi a lokacin da yake gwamnan jihar.
Abban na Kanawa ya yi wannan furuci ne a jawabinsa bayan ta tabbata cewa shi ne zababben gwamnan Kano.
Yayin da yake yi wa Kanawa godiya da suka danka masa amanarsu a hannunsa, ya ce su sha kuruminsu don ba za su yi nadama ba.
Sabon zababben ya ce zai gudanar da gwamnatin da za ta fifita maslahar al’umma da kuma kyautata ilimi.
Ya ce al’ummar jihar sun nuna masu kauna a lokacin da yake ya kin neman zabe da kuma a ranar zabe, duk bai dauki salon amfani da abin duniya ba wajen neman kuri’unsu.
“Muna godiya da Allah da Ya ba mu wannan nasara.
“Duk da kalubalen da aka fuskanta kama daga tambarin jam’iyyar mu da ya yi dishi-dishi a takardun zabe, da yadda abokan hamayyar mu suka yi amfani da abin duniya don a kada musu kuri’a, ya kara tabbatar mana da cewa ‘Taliya ba ta zabe’.
Ya kara da cewa ba zai yi sako-sako wajen yaki da cin hanci da kyautata rayuwar al’umma ba.
Haka kuma, ya ce zai bayar da fifiko wajen kyautata ilimi da lafiya da kasuwanci da tsaro da harkokin noma.
Abba Gida-gida ya ce cikin kwanaki 100 na farkon mulkinsa zai yi kokarin inganta bangaren ilimin jihar.
Abba Gida-gida – wanda tsohon kwamishinan ayyukan ne zamanin mulkin Kwankwaso – ya alkawarta cewa zai karasa duk ayyukan da gwamnatin jihar ta yanzu ta faro matukar za su amfanar da al’ummar jihar.
A ranar Litinin ce Hukumar Zabe ta Kasa INEC ta bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar Asabar.
Sabon zababben gwamnan ya lashe zaben da aka gudanar da kuri’u miliyan 1,019,602, bayan doke babban abokin hamayyarsa, Mataimakin Gwamnan Kano, Nasiru Gawuna na jam’iyyar APC mai mulkin jihar, wanda ya samu kuri’u 890,705.