Tsohon shugaban ƙasar Amurka Donald Trump na fuskantar tuhume-tuhume kan zargin da ake masa na biyan wata tsohuwar ƴar wasan batsa Stormy Daniels kuɗi domin ta ɓoye mu’amalar da suka yi.
Ms Daniels ta yi iƙirarin cewa Mista Trump ya kwanta da ita, kuma ta karɓi kuɗi $130,000 daga hannun tsohon lauyansa kafin zaɓen 2016 domin kada ta fallas shi.
Daga baya an ɗaure lauyan, Michael Cohen, bisa wasu zarge-zarge.
Tsohon shugaban ƙasar ya musanta cewa ya yi lalata da Miss Daniels tun bayan zargin da aka yi masa a shekarar 2018.
Mun yi mu’amala da mista Trump a ɗakin otal’
Miss Daniels, wadda ainihin sunanta Stephanie Clifford, ta bayyana wa manema labarai cewa ta haɗu da Mista Trump a lokacin wata gasar wasan golf a watan Yulin 2006.
Ta yi zargin cewa sun sadu sau ɗaya a ɗakin otal ɗin sa da ke bakin ruwa na Tahoe, wani wurin shakatawa tsakanin California da Nevada. Sai dai lauyan mista Trump ya musanta zargin a lokacin.
“Da alama bai damu da lamarin ba. Ya kasance mai girman kai,” in ji Miss Daniels, yayin da take amsa tambayar da wata mai hira ta yi mata cewa ko Mista Trump ya ce ta yi shiru game da zargin yin lalata.
Mai ɗakin Mista Trump a lokacin, Melania Trump, ba ta halarci gasar ba kuma ta haihu a lokacin.
Daga baya mai magana da yawunsa ya ce ba a sanar da su batun wata tuhuma da ake masa ba.
A farkon wannan shekarar ne, mai shigar da kara na birnin New York Alvin Bragg, ya kafa wani kwamitin alkalai da zai binciki ko akwai isassun shaidun da za su iya sa a gurfanar da tsohon shugaban ƙasar kan kuɗaɗen da aka biya miss Daniels.
Shi ne wanda zai yanke hukunci ko za a yi tuhuma ko a’a, idan an gabatar da shi.
Wani kwamitin lauyoyi na gudanar da wani zama na sirri, kuma mai gabatar da kara ya kafa shi ne domin tantance ko akwai isassun shaidun da za su iya sa a tuhumi Trump.
Idan aka gabatar da tuhume-tuhumen, zai zama shari’ar laifi ta farko da aka taɓa yi wa wani tsohon shugaban Amurka.
A shafinsa na sada zumunta, Truth Social, Mista Trump ya kira binciken da aka masa a matsayin bi-ta-da-kullin siyasa da tsarin shari’a da ke cike da cin hanci ke yi a kansa.