Barau Jibrin ya tsaya takarar shugabancin majalisar dattawa

0
97

Barau na jam’iyyar APC, ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a lokacin da yake zantawa da manema labarai a zauren majalisar da ke Abuja.

Ya ce: “Ina da niyyar zama Shugaban Majalisar Dattawa ta 10 da yardar Allah, nan da ’yan kwanaki ko makonni zan bayyana a hukumance.”

Sanatan na Kano ta Arewa, ya ce shi ne ya fi kowa kwarewa a cikin wadanda ke neman ofishin shugaban na majalisa ta 10.

Ya ce ya kamata a yi la’akari da yankin Arewa maso Yamma don zabar Shugaban Majalisar Dattawa duba damwanda ya bai wa zababben Shugaban kasa kuri’u mafi yawa.

Barau, ya ce bai kamata a yi duba da Addini ba wajen zabar sabon shugaban majalisar ta 10 ba.

Sanatan ya ce, ‘’Majalisar dokoki wani bangare ne na gwamnati wanda zai yi la’akari da wanda zai iya aikin.

“Majalisar dokoki ta kasa tana da damar daidaita ayyukanta a matsayin wani bangare na gwamnati, shi ya sa muke da ka’idojinmu.

“A bayyane yake a cikin tsarin majalisar dattawa cewa zaben kujerar shugaban majalisar dattawa zai fi dacewa da wanda ya fi gogewa.

“Daga cikin wadanda ke neman  wannan mataki, ni ne na fi kowa matsayi kuma na fi kwarewa.

“Al’amarin dai shi ne cancanta, akwai bukatar mutum ya samu kwarewa kafin ya zama shugaban majalisar dattawa.

“Ina daya daga cikin wadanda ke burin zama shugaban majalisar dattawa ta fuskar kwarewa.

“Shin yanzu kuna son kawo koma baya ga cancanta? Akwai lokacin da muka yi Shugaban Majalisar Dattawa Kirista, David Mark, da mataimakinsa, Ike Ekweremadu, wanda shi ma Kirista ne da kuma kakakin Majalisar Wakilai, Patricia Etteh, ita ma Kirista ce.

“Kawo maganar Addini cikin wannan lamari bai dace ba, magana ake yi cancanta.

“Idan magana ake ta gogewa, to ni ne na fi kwarewa.”

Ya kuma ce, “Akwai bukatar bai wa yankin Arewa maso Yamma fitar da shugaban majalisar dattawa saboda mun bai wa zababben shugaban kasa kuri’u mafi yawa.

“Muna son shugaban kasarmu ya sake tsayawa takara a karo na biyu, mun ga abin da ya yi a Legas kuma muna son ya maimaita hakan a fadin kasar nan.

“A shekarar 2015, lokacin da aka ayyana shugaba Buhari a matsayin wanda ya lashe zabe, ya yi kokarin bayar da kulawa ga yankin da ya ba shi kuri’u masu yawa, an ware muhimman mukaman gwamnati zuwa Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas domin a bai wa jama’a dama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here