Za a tashi da azumin Ramadan ranar Alhamis – Saudiyya

0
82

Kasar Saudiyya ta sanar da cewa, ranar Alhamis 23 ga Maris a matsayin ranar farko ga watan Ramadan 2023.

Sanarwar da fadar masarautar kasar ta fitar, ta ce kwamitin ganin jinjirin watan, bai ga alamun kamawar sabon watan ba.

Masallatan Harami su ma sun tabbatar da wannan labari, inda suka ce: “Ba a ga jinjirin watan #Ramadan1444 ba a Saudiyya saboda haka ranar Alhamis, wato 23 ga Maris 2023 za ta zama ranar farko ta Ramadan 1444.”

Kasashe da dama sun sanar da ranar Alhamis a matsayin ranar farko ga watan Ramadan.

Ramadan, daya daga cikin rukunan Musulunci, shi ne wata na tara a kalandar Musulunci. A cikin watan Musulmai suna azumi tun daga ketowar alfijir zuwa faduwar rana, wato su na kaurace wa sha, da ci.

Musulmai da dama ne ke ziyartar kasar Saudiyya a cikin watan Ramadan domin gudanar da aikin Umrah.

Ba kamar aikin Hajji ba, ana iya yin Umra a kowane lokaci na shekara. Da yawa sun fi son yin aikin Umra a cikin Ramadan.

Rahotanni sun nuna cewa mutane miliyan hudu ne suka gudanar da aikin Umrah a cikin kwanaki 20 na farkon watan Ramadan na shekarar da ta gabata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here