INEC ta ayyana 29 ga Maris a matsayin ranar zaben cike gurbi a Adamawa

0
288

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), ta ayyana ranar Laraba 29 ga watan Maris a matsayin ranar da za ta sake gudanar da zaben kujerar gwamna a wasu akwatinan 39, domin ciki gurbin zaben a Jihar Adamawa.

INEC ta sanar da zaben kujerar gwamna da ta gudanar ranar Asabar a jihar a matsayin bai kammalu ba, domin kuri’un da aka soke sun fi wanda dan takarar da ke kan gaba a zaben ya samu.

Ta ce dan takarar kujerar gwamna karkashin jam’iyyar PDP kuma gwamnan jihar, Ahmadu Umaru Fintiri, ya samu kuri’u 421,524, sai ‘yar takarar kujerar gwamna a jam’iyyar APC, Aishatu Dahiru Binani ta zo na biyu da kuri’u 390, 275.

Farfesa Muhammad Mele, ya ce hukumar za ta sake zabe a cibiyoyin kada kuri’a 69, da aka soke zabensu, da suke da kuri’u 41,796, da katin zabe dubu 37,016.

Sai dai a wani taron manema labarai, mataimakin shugaban kwamitin yakin neman zaben jam’iyyar PDP a jihar, Felix Tangwami, ya zargi kwamishinan INEC na jihar Barista Hudu Yunusa Ari, da kara yawan cibiyoyin zuwa 77.

Ya kara da cewa “Wannan ba za mu amince da shi ba, mun bukaci lauyoyinmu da su dauki mataki, domin bai kamata a maishe mu da jiharmu, wajen wasan kwaikwayo ba.

“Muna kira ga jami’an tsaro masu sa ido kan zabe, ‘yan jaridu da jama’a, da su sa ido da matsawa hukumar INEC da ta cire kwamishinan hukumar Hudu Yunusa, domin ba mu da amince da shi, bai zama mutum mai gaskiya ba” in ji Tangwami.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here