Kungiyar kwadagon Najeriya za tayi zaman dirshan a bankin CBN

0
307

 

Kungiyar Kwadago ta Najeriya NLC, ta umurci dukkan ma’aikata da su fara mamaye dukkanin rassan ofisoshin babban bankin Najeriya a fadin kasar daga mako mai zuwa, kan matsalar karancin takardun kudi da ake fama da ita a kasar.

Shugaban kungiyar, Joe Ajaero ne ya bayar da umarnin, yayin wani taron manema labarai da kungiyar ta gudanar a Abuja.

Wannan na zuwa ne, bayan cikar wa’adin mako guda da aka ba wa babban bankin na ya

samar da tsabar kudi ga ‘yan Najeriya.

Rashin isassun takardun kudi ya jefa al’ummar Najeriya da dama cikin mummunan yanayi, yayin da ‘yan kasuwa ke ci gaba da koka wa da kuma kira ga gwamnati, da ta kawo musu daukin gaggawa.

Biyo bayan furucin da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya yi na cewa bai nemi babban bankin Najeriya CBN da kuma babban lauyan gwamnatin tarayya da su bijirewa umarnin kotun koli ba, babban bankin ya bayyana cewa za a iya ci gaba da amfani da tsoffin takardun kudi na Naira 200, 500 da kuma 1,000.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here