suwar da ke kara farashin kayayyaki saboda zuwan azumi da su daina saboda ya saba da koyarwar Musulunci.
Ya bayyana haka ne ranar Laraba, a cikin sakonsa ga al’ummar Musulmi kan shiga watan Ramadan da aka fara ranar Alhamis.
Buhari, ya kuma shawarci Musulman Najeriya da su yi amfani da lokacin wajen haskaka kyawawan dabi’un addinin Musulunci a mu’amalolinsu, ba wai kawai a baki ba.
Sanarwar, wacce Kakakin Shugaban, Malam Garba Shehu ya fitar, ta ce, “Ya kamata mu yi amfani da wannan lokacin wajen bayyana kyawawan dabi’un Musulunci irin su tausayi da kaunar juna.
“Wannan lokaci ne na komawa ga Allah da kuma jin tsoronSa, ta hanyar guje wa duk abin da zai cutar da dan Adam.
“Ramadan wata ne na kamewa daga barin ci da sha tun daga hudowar Alfijir har zuwa faduwar rana, kuma yana daidaita talaka da mai kudi a wajen jin yunwa, ta yadda kowa ke zama daya.
“Ina sane da yadda wasu ’yan kasuwa ke kara farashin kayayyaki, ciki har da na kayan abinci, a kowanne watan Ramadan. Yin hakan ya saba da ainihin manufar azumin da ma ta Musulunci,” in ji Buhari.
A ranar Alhamis ce Musulmin Najeriya suka bi sahun takwarorinsu na sauran sassan duniya domin fara azumin watan Ramadan, bayan an ga watan a wurare da dama na kasar.