Ciwon zuciya na kama ’yan Najeriya 80,000 duk shekara – ACTSON

0
128

Kungiyar likitocin zuciya ta Najeriya (ACTSON) ta ce sama da mutum 80,000 ne suke bukatar a yi musu aiki sakamakon kamuwa da ciwon zuciya kowacce shekara a fadin Najeriya.

Shugaban kungiyar, Dokta Uvie Onakpoya, ne ya bayyana hakan ranar Lahadi a Abuja, yayin babban taron kungiyar na shekara-shekara karo na biyar.

Ya lura cewa ciwon zuciya na kan gaba wajen kisan mutane a duniya, kuma adadin wadanda ku mutuwa a sakamakon shi ya haura na dukkan ragowar cututtuka baki daya.

Dokta Uvie ya ce yayin da wasu daga cikin nau’ukan cutar da su ake haifar mutum da su, wasu kuma a kan kamu da su ne dalilin kwayoyin cuta da yanayin rayuwa da hawan jini da dai sauran dalilai.

Shugaban kungiyar ya kuma ce a cikin kowanne yara 100, a kan haifi akalla takwas dauke da cututtuka masu alaka da ciwon zuciya kamar rami a cikin zuciyar.

Kazalika, ya ce a kowacce shekara, a kan haifi akalla jarirai 55,000 da ciwon zuciya.

Ko a bara, shugaban ya ce mutum 212 kawai aka iya yi wa tiyatar ciwon zuciya sakamakon tsadar da aikin yake da ita, adadin da ya ce ya yi kasa sosai idan aka kwatanta da yawan masu bukatar sa.

Sai dai ya ce kungiyar na kira ga hukumomin kasar da su yi dokar da za ta saukaka aikin ciwon zuciya ta yadda ’yan Najeriya za su same shi cikin rangwame a asibitocin gwamnati da masu zaman kansu.

A yayin taron, Uwargidan Shugaban Kasa, Hajiya Aisha Buhari, wacce hadimarta, Dokta Victoria Ogala-Akogwu ta wakilta, ta ce a kwanan nan, ta dauki nauyin aikin zuciya ga yara 10 da kuma manya 13.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here