Martanin Oyedepo akan zargin maganar da suka yi da Obi ta waya

0
87

Shugaban cocin Living Faith Worldwide, Bishop Oyedepo ya ce bai taba yi wa wani dan siyasa kamfe ba, ko kuma kokarin shawo kan wasu al’umma su zabi wani ba.

Ya fadi hakan ne a lokacin da yake yin huduba a cocin tasa da ke da cibiya a yankin Ota na jihar Ogun a ranar Lahadi.

Ya ce “Ban taɓa yi wa wani kamfe ba ko kuma yi ma wasu magana a madadin wani ba, kuma ba zan taɓa yi ba har na mutu.”

Sai dai babban limamin Kiristan bai ambato batun muryarsa da aka ji a hira da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here