Mata dubu 800 na rayuwa da cutar yoyon fitsari a Najeriya – Rahoto

0
128

Asusun kula da yawan jama’a na Majalisar Dinkin Duniya UNFPA ya bayyana cewa akwai mata fiye da dubu 800 da ke rayuwa da cutar yoyon fitsari a sassan Najeriya da kaso mai yawa a arewacin kasar.

Shugaban ofishin na UNFPA reshen jihar Adamawa Dr Danladi Idrissa a jawabinsa yayin yaye mata 50 da suka warke daga cutar ta yoyon fitsari ya ce fiye da rabin masu kamuwa da wannan lalurar ta yoyon fitsari na arewacin kasar wanda ke da nasaba da al’adun al’ummar yankin.

Dr Idrissa ya bayyana cewa mata 225 cikin 265 da aka yiwa aikin yoyon fitsari sun warke garau karkashin jagorancin asusun na UNFPA da gidauniyar Fistula da kuma hadin gwiwar ma’aikatar kula da harkokin mata a Najeriyar.

A cewar kwararren likita akwai mata 40 da ke bukatar tiyata ta musamman wadanda rashin kayan aiki a jihar Adamawa ya hana iya aiwatar da tasu tiyatar.

Masana kiwon lafiya na alakanta cutar ta yoyon fitsari ga mata da auren wuri baya ga doguwar nakuda a gida, dalilan da ake ganin su ne kan gaba wajen haddasa lalurar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here