Chelsea ta nemi gafara kan miyagun kalaman da magoya bayan ta suka yi wa Liverpool

0
116

Chelsea ta yi tir da ba’ar da magoya bayanta suka yi wa ‘yan wasan Liverpool kan wani bala’in da ya taba faruwa da kulob din a Hillsborough.

Sanarwar da Chelsea ta fitar ta ce wasan kwallon kafa bai lamunci wakar kin jini ba tana mai neman afuwa daga duk wanda lamarin ya batawa rai a karawar da suka yi a Stamford Bridge inda suka yi canjaras.

Ita ma Liverpool ta ce dole a daina yi mata kalami maras dadi kan bala’in da ya fada wa kulob din a 1989 inda mutum 97 suka mutu a wasan kusa da na karshe na gasar FA.

Ba yanzu aka fara irin wadannan kalamai ba. Ko a bara ma sai da kocin Manchester City, Pep Guardiola, ya nemi afuwa game da yadda magoya bayan kulob dinsa suka yi wakar kiyayya game da bala’in da ya faru a shekarar ta 1989.

Chelsea, da ta kori kociya biyu cikin watanni saboda rashin nasara, ba ta yi nasara ba a karawarta da Liverpool inda suka yi canjaras.

Kungiyar tana mataki na 11 da maki 39 a teburin gasar Firimiya yayin da Liverpool take ta 8 da maki 43.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here