Dan jaridar da aka kora saboda caccakar gwamna Zulum ya sami aiki a babbar kafar labarai a kasar waje

0
111

Zargin caccakar Gwamna Babagana Umara Zulum na Jihar Borno ya jefa wani dan jarida ya rasa aikinsa nan take sakamakon harzuka Gwamnan da ya yi.

Rahotanni sun ce dan jaridar, mai suna Malam Adamu Ngulde da ke aiki a wani gidan rediyo mai zaman kansa da ake ce da shi Al-Ansar cikin Jihar ya karbi takardar dakatarwar ce daga mahukuntan tashar.

Sai dai daga bisani, sabuwar kafar yada labarai ta kasar Turkiyya TRT ta ba shi aiki a matsayin wakilinta mai kula da Jihohin Borno, Yobe da Adamawa.

Takardar ta ce an sallame shi daga aiki ne sakamakon korafin da Gwamnan ya yi a kan caccakarsa da Adamu Ngulde ya yi a cikin wani shirin sa da ake ce da shi ‘Arewa ina mafita’.

Kamar yadda wasu rahotanni ke cewa, Gwamna Zulum ya yi ikirarin cewa a cikin wani shiri na musamman na rediyo a harshen Hausa, Arewa Ina Mafita? ne dan jaridar ya caccaki Gwamnatin sa ba tare da yi masa adalci ba musamman ta wajen rashin kokarin duba lamarin kamar yadda tsarin aikin jarida ya tanada.

A cewar Gwamnan, da gangan aka kasa samun daidaito a cikin shirin da nufin tozarta gwamnatinsa.

Gwamna Zulum ya kuma bayar da umarnin rufe tashar daga ci gaba da yada shirye-shirye har illa masha Allahu.

Gwamnan ya ba da umarnin ne nan take a makon da ya gabata yayin da ya karbi bakuncin wasu jami’an hukumomin gudanarwar kafafen yada labarai a jihar a ziyarar taya murna bayan sake zabensa a karo na biyu a zaben Gwamnan da aka gudanar a watan da ya gabata.

Sai dai duk da wannan umarni na rufe gidan rediyon, amma ya ci gaba da gudanar da ayyukansa har bayan faruwar lamarin inda majiyoyin suka yi zargin cewa mahukuntan gidan sun nemi gafarar Gwamnan, wanda hakan ya sa ya janye matakin da ya dauka cikin lokaci.

Amma Wata majiya na cewa dan jarida Adamu Ngulde wadda shi ne mai gabatar da wannan shiri na Arewa ina Mafita da Gwamnan ke korafi a kai, ya ambata cewa Babban Manajan tashar ya umarce shi da ya ajiye aikinsa ba tare da sanin kwamitin amintattun gidan ba.

Don haka ya yi zargin cewa Manajan ne ya yi gaban kansa wajen sallamarsa daga aiki duk da cewa ba shi kadai ne ke gabatar da wannan shirin.

Da Aminiya ta tuntubi dan jaridar kan matakin sallamar tasa, sai ya ce abincinsa ne ya zo karshe a gidan, kuma ya rungumi kaddara.

Ngulde ya kuma ce a matsayinsa na Musulmi, ya karbi wannan lamari a matsayin kaddara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here