Shin Messi na shirin bin Ronaldo Saudiyya?

0
109

Alamu sun nuna cewa Lionel Messi na shirin barin Paris Saint-Germain a karshen kaka. Domin kuwa akwai kulob-kulob din da ke taya tsohon dan wasan na Barcelona, mai shekara 35.

Bayanai sun ce tsohon kulob dinsa na daga kungiyoyin da ke kan gaba wurin neman dan wasan, amma kuma kulob din nan na kasar Saudiyya Al Hilal ya yi wa dan wasan tayi mai tsoka.

Fabrizio Romano, dan jarida mai sharhi kan wasanni, ya bayyana cewa Al Hilal ta yi wa Messi tayin sama da fam miliyan 400 a duk shekara. Sai dai ya ce alamu sun nuna Messi ya fi son ya ci gaba da taka leda a Turai.

Ganin cew kulob din nan na Saudiyya Al Nassr ya dauki tsohon dan wasan Manchester United Cristiano Ronaldo a bana, ana ganin shi ya sa abokan hamayyarsu wato Al Hilal su ma suke so su samu dan wasa mai kwari kamar Messi.

Kwantiragin Messi dai za ta kare a PSG a watan Yuni, kuma duk da kulob din yana so zakaran Kofin Duniya na 2022 din ya tsaya kulob din, amma har yanzu Messi din bai ba su amsa kan lamarin ba inda yake son su ba shi garanti kan lamuran da suka shafi hada-hadar kudi da kuma zamansa a kulob din.

Al Hilal dai na son biyan Messi kudin da suka kusan ninka wanda Al Nassr ta sayi Ronaldo, amma duk da wannan tayi mai tsoka rahotanni na nuna cewa ba lallai Messin ya koma Saudiyya ba domin iyalansa ma na son ya koma Barcelona, kulob din da ya daga sa a duniya.

Wani dalili da kuma zai iya sa Messi ya bar PSG shi ne dangantakarsa da magoya bayan kulob din. Magoya bayan PSG sun rinka yi wa Messi eho! Bayan da kulob din ya yi rashin nasara a hannun Lyon da ci 1-0.

A yayin wasan, Messi ya samu damar cin kwallo sau 26 amma bai samu sa’a ba. Ana ganin har da rashin nasarar da PSG din ta yi ne a wasanta na baya da Rennes ne ya kara bata wa magoya bayan na PSG rai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here