ranar Larabar nan aka yi jana’izar Hajiya Ladi, matar Gwamna Jihar Kano na farko, Alhaji Audu Bako, wadda ta rasu tana da shekara 93.
Hajiya Ladi wadda ta rasu bayan fama da jinya, an gudanar da jana’izarta ne a Fadar Sarkin Kano, bayan ta rasu a wani asibiti da ke Kano.
Limamin Fada, Malam Mu’awiya Baba Yaro ne ya jagoranci sallar jana’izar, da da misalin karfe 1.50 na rana kafin a kai gawar Makabartar Dandolol da ke Kano.
Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero da sauran sarakai da manyan mutane sun halarci jana’izar