‘Yan sandan kasar Isra’ila sun kai hari cikin Masallacin Kudus

0
96

Akalla makaman roka tara ne aka harba kan garuruwan kudancin Isra’ila daga gaza a cikin daren da ya gabata, bayan da ‘yan sandan Isra’ila suka kai hari kan masu ibada a Masallacin Birnin Kudus.

‘Yan sandan sun ce sun kai harin ne a matsayin martani ga masu zanga-zanga.

Hukumomin Falasdinu sun gaya wa BBC cewa makaman rokar akalla guda tara ne aka harba yankunan na aIsra’ila, a matsayin wani martani na farmakin da ‘yan sandan Isra’ilar suka kai kan Musulmi da ke ibada a cikin kwaryar Masallacin na Kudus a yankin gabashin birnin da ta mamaye.

Babu dai wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin, amma ana ganin Hamzas ce ta bayar da umarnin.

Wadanda suka ga yadda abin ya faru sun ce ‘yan sandan Isra’ila sun yi amfani da gurneti-gurneti da harsasai na roba domin tarwatsa Musulmi Falasdinawa da ke ibada a cikin kwaryar masallacin su fita.

Sai dai a nasu bangaren ‘yan sandan Isra’ila sun ce ala tilas suka shiga Masallacin saboda masu zanga-zanga da suka rufe fuskokinsu suka fake suka kuma kulle kansu a ciki.

Sannan suna dauke da abubuwan tartsatsin wuta da sanduna da duwatsu in ji ‘yan sandan.

Sanarawar ‘yan sandan ta ce lokacin da jami’ansu suka shiga sai aka rika jefa musu tartsatsin wutar ana kuma jifansu da duwatsu daga cikin.

Suka ce a hakan ne ma har wani jaimin dan sanda ya ji rauni a kafa.

Kungiyar agaji da Red Crescent ta bayar da rahotannin cewa an jikkata Falasdinawa 14, kuma lokacin da jami’anta na lafiya suka yi kokarin shiga ciki jami’an tsaron Isra’ila sun hana su shiga Masallacin.

Kakakin shugaban hukumar Falasdinawa ya yi Allah-wadarai da harin na Isra’ila yana mai cewa , daman sun gargadi masu mamayen da kada su keta haddin wurin su shiga wuraren ibada masu tsarki na Masallacin, wanda hakan zai iya haddasa mummunan rikici.

Jagoran kungiyar Hamas ta Falasadinawa Ismail Haniyeh, ya ce abin da ake yi a masallacain mai tsarki na Kudus laifi ne da ba a taba yin irinsa ba kuma Israila za ta yaba wa aya zaki a kai.

Hotunan bidiyo da ake ta yadawa a shafukan intanet na nuna yadda yan sandan Isra’ila ke dukan Falasdinawa a cikin Masallacin.

A shekarar 2021 Hamas, wadda ke mulki a Gaza, ta rika harba makaman roka zuwa sassan birnin Kudus inda Yahudawa suke sakamakon irin wannan farmaki a Masallacin bayan rikici da aka shafe makonni ana yi a birnin abin da ya haifar da yaki na kwana 11 da Isra’ila

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here