An cafke wata mata bisa zargin sace tumatir

0
104

Jami’an hukumar tsaron farin kaya (NSCDC) reshen Jihar Kwara, sun kama wata mata ‘yar shekara 32 mai suna Mariam Yusuf, bisa zarginta da sace kwandon tumatir da tattasai a fitacciyar kasuwar da ke garin Ilorin, babban birinin jihar.

Wadda ake zargin, jami’an NSCDC sun cafke ta ne a ranar Laraba bayan da suka bi diddigin zargin cewa an sace kwandon tumatir da tattasai a kasuwar ta Kulende da ke a garin Ilorin.

Kakakin hukumar NSCDC na jihar, Ayeni Olasunkanm, ya tabbatar da kama matar a cikin sanarwar da ya fitar a yau Alhamis, inda ya ce wadda ake zargin ta amsa laifinta kuma nan ba da dadewa ba za a gurfanar da ita a gaban Kotu.

Ya bayyana cewa, jami’an NSDCD ne suka kamata a ranar 5 ga watan Afirlu, bayan an samu rahoto daga wajen wasu ‘yan kasuwar.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here