Ba da gangan ba ne jinkirin shari’ar Alhassan Doguwa kan zargin kisan kai – Gwamnatin Kano

0
137

Gwamnatin jihar Kano ta mayar da martani a kan zargin da wasu ‘yan fafutuka ke yi cewa ta ƙi gurfanar da shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai a gaban kotu.

‘Yan sanda sun kama Alhassan Ado Doguwa a ƙarshen watan Fabarairu, inda suka kai shi kotun majistare bisa zargin ya harbi wasu mutane, kwana ɗaya bayan zaɓen shugaban ƙasa a mazaɓarsa ta Doguwa/Tudun wada.

Sun kuma tuhumi ɗan majalisar wakilan da kashe mutum uku, da raunata wasu takwas a ƙaramar hukumar Doguwa lokacin da ake karɓar sakamakon zaɓe.

Kotun dai, ta ba da umarnin a ci gaba da tsare wanda ake zargin a gidan yari, kafin fara shari’a gadan-gadan.

Amma an ga shugaban masu rinjayen a cikin wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta kafin ‘yan sanda su kama shi, yana musanta zarge-zargen haddasa tashin hankali a lokacin zaɓen.

Sai dai, kwana ɗaya kafin a mayar da shi kotun majistare, sai wata babbar kotun tarayya a Kano ta bayar da belin ɗan siyasar ranar 6 ga watan Maris.

Tun daga lokacin kuma ba a sake jin batun komawa don ci gaba da shari’ar ba.

Lamarin dai ya sa ɓangarori da dama sun fara zargin ko hukumomi a Kano, na ƙoƙarin danne maganar, har ta bi ruwa.

To amma a martanin da ta mayar ranar Laraba, ma’aikatar shari’ar jihar Kano ta ce ba da gangan, ta ƙi kai shi kotu ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here