Gwamnatin tarayya ta amince da fitar da kudi Naira Biliyan N320,345,040,835 a matsayin kudin tallafin Gine-gine a makarantun gwamnati a fadin kasar nan na shekarar 2023.
Babban Sakataren zartaswa na Asusun tallafin manyan makarantun gwamnati (TETFund), Arc. Sonny Echono, ya bayyana hakan a Abuja a ranar Laraba, yayin wani taron karawa juna sani na shekara-shekara tare da dukkan shugabannin makarantun da suka amfana da tallafin.
Echono ya ce, taron wata hanya ce ta jin ra’ayoyi da kuma tantance ayyukan da TETFund ta yi na bayar da tallafi wajen ganin an samu inganci a bangaren bayar da tallafin.
Ya bayyana cewa, kowace jami’a za ta samu, jimillar kudi naira biliyan N1,154,732,133.00 a yayin da kowace Kwalejin Kimiyya da fasaha za ta samu jimillar kudi Naira Miliyan N699,344,867.00, sai kowace Kwalejin Ilimi za ta samu jimillar kudi naira miliyan N800,862,602.
A nasa jawabin, babban sakataren ma’aikatar ilimi ta tarayya, David Adejo, ya bukaci makarantun da suka ci gajiyar tallafin da su yi amfani da kudaden ta hanyar da ta dace cikin adalci, yana mai cewa kasar nan ba ta bukatar aiki a takarda.