Jirgin ruwa dauke da mutane ya yi hatsari a tsakiyar kogi a Bayelsa

0
129

Wani jirgin ruwa dauke da fasinjoji ya yi hatsari a tsakiyar Kogin Okoroma da ke Karamar Hukumar Nembe ta Jihar Bayelsa.

Rahotanni daga jihar sun ce a halin yanzu mutum bakwai sun bace bayan hatsarin jirgin ruwan da ya dauko fasinjojin daga Yenagoa zuwa yankin Okpoama da ke Karamar Hukumar Brass.

Jirgin katakon na dauke da lodin fasinjoji da kaa ne a lokacin da hatsarin ya auku, ya fara nutsewa a tsakiyyar Kogin Okoroma.

Kawo yanzu wasu magidanta da ma’aikatan ceto na kokarin gano wadanda ba a gani ba bayan hatsarin jirgin ruwan.

Ba a kai ga samun alkaluman mutanen da hatsarin ya ritsa da su ba, amma Shugaban Ma’aikatan Kula da Lafiyar Teku na Jihar Bayelsa, Ipigansi Ogoniba, ya ce jami’ansu na gudanar da aikin ceto, kafin tattara alkaluma.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here