Rundunar ‘yan sanda ta cafke jami’inta bisa halaka wani dan kasuwa

0
135

Rundunar ƴan sandan jihar Delta ta cafke wani jami’inta bisa zargin aikata laifin halaka wani ɗan kasuwa, ana tuhumar jami’in ɗan sandan da laifin halaka wani ɗan kasuwa har lahira bayan ya ƙi bashi cin hanci, rundunar ƴan sandan ta bayar da tabbaci wajen ganin cewa ta yi wa iyalan mamacin adalci.

Rundunar ƴan sandan jihar Delta ta kama Insfetan ƴan sanda, Obi Abri, bisa zargin halaka wani ɗan kasuwa, Onyeka Ibe, a wurin duba ababen hawa kan titin Ugabolu-Illah a birnin Asaba na jihar. Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, DSP Edafe Bright, ya bayyana hakan a wani dogon rubutu da yayi a shafin sa na Twitter ranar Laraba.

A rubutun na sa mai taken ‘Zargin kisan wani Onyeka Ibe’ Edafe ya rubuta cewa:

“An gano insfetan ɗan sandan, an cafke shi, an taso keyar sa sannan an tsare shi.

“Rundunar ƴan sanda tana bayar da tabbacin ga al’umma da iyalan mamacin zata yi adalci.”

“An fara gudanar da bincike sannan za tura shi zuwa kotun domin fuskantar tuhuma.

Yadda dan kasuwan ya rasa ransa 

Jaridar Punch ta samo cewa Onyeka da matarsa suna kan hanyar su ta zuwa wani waje a jihar lokacin da wasu ƴan sanda suka tsayar da motar su a wani wajen duba ababen hawa.

Bayan sun tsayar da su, ɗaya daga cikin ƴan sanda ya nemi Onyeka ya bashi N100, wacce ya kuma bashi ɗin. Bayan ya bashi naira ɗarin, sai ɗan sandan Obri Abri ya sake zuwa masa da buƙatar ya ƙara masa wasu kuɗin amma sai ɗan kasuwar ya ƙi.

Hakan ya sanya cece-kuce ya ɓarke a tsakanin su wanda yayi munin da har ta kai Abri ya harbi Onyeka a kansa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here