Buhari ya gaza gudanar da sahihin zabe a 2023 – Kwankwaso

0
128
Rabiu-Musa-Kwankwaso-
Rabiu-Musa-Kwankwaso-

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP a zaben 2023, Sanata Rabi’u Kwankwaso ya zargi Shugaban kasa Muhammadu Buhari da gaza gudanar da sahihin zabe a 2023.

Ya ce shugaban kasar bai yi abin da ya dace ba don ganin an gudanar da sahihin zabe.
Ya kuma zargi jam’iyyar APC mai mulki da yin magudin zabe a wasu jihohi, musamman zaben shugaban kasa.

Kwankwaso ya yi zargin cewa sakamakon zaben da aka kammala ba zabin ‘yan Nijeriya ba ne.

Da yake magana a taron farko bayan zaben 2023 na majalisar zartaswar jam’iyyar NNPP ta kasa, tsohon ministan tsaro kuma tsohon gwamnan Jihar Kano har sau biyu ya koka da yadda ‘yan Nijeriya ba su sami damar cin moriyar canji mai kyau da suke nema ba.

Ya kuma bayyana cewa ‘yan Nijeriya sun gaji da jam’iyya mai mulki, domin ya ci gaba da cewa APC ta koma sayen kuri’u da kudaden gida da na waje, da kuma yin amfani da ‘yan daba wajen murkushe ‘yancin zabe.

Sanata Kwankwaso ya yi kira na musamman ga Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje, wanda ya zarga da shigo da ‘yan daba daga jihohi da kasashe makwabta, kamar yadda ya kuma yi nuni cewa akwai sa hannun wasu jami’an tsaro a tashe-tashen hankula da suka shafi zabe.

A yayin da yake zargin ‘yan siyasa da cewa da gangan suke talauta ‘yan Nijeriya domin su sayi kuri’a a lokacin zabe, ya yi gargadin a guji cin nasara ko ta halin kaka, domin ya koka da yadda rashin adalci ke haifar da ‘yan fashi, Boko Haram, da sauran rikice-rikicen da suka addabi kasar nan.

Jagoran NNPP na kasa ya yi nadamar cewa akwai abubuwa da yawa da ke damun dimokuradiyyar Nijeriya. Inda ya ce mutane kalilan ne ke amfana da tsarin.

Yayin da yake gargadin cewa, “Nijeriya tamu ce kuma babu wanda ya isa ya kore mu a ciki “, jagoran ya bayyana fatansa cewa bangaren shari’a ya kasance wuri mafi kyau a gare mu duka.”

Ya yi kira ga shugabannin jam’iyyar NNPP da su yi amfani da damar da aka ba su kafin zaben 2027, su zage-dantse wajen gudanar da ayyukan da suka dace a mazabarsu.

Hakan na zuwa ne yayin da ya yi kira ga Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da ta inganta harkokinta wajen gudanar da zabuka a nan gaba, inda ya koka da yadda ba a buga tambarin jam’iyyar a kan takardun zabe ba, don haka ya sa jam’iyyarsa ta rasa kuri’an magoya bayanta a wasu wurare.

Ya bayyana cewa hatta wasu masu sa ido na kasa da kasa sun kasa tantance tambarin jam’iyyar NNPP da ke cikin takardun zabe.

Don haka, ya yaba wa jam’iyyar bisa nasarorin da suka samu, inda ya bayyana cewa mutane da dama ne ke neman shiga kafin zaben 2027.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here