Kusan mutum 50 sun mutu a harin da aka kai Benuwai

0
117

Hukumomi a Jihar Binuwai da ke yankin tsakiyar Nijeriya sun ce akalla mutum 50 sun mutu sakamakon hare-haren da ‘yan bindiga suka kai wani kauye na jihar.

Shugaban karamar hukumar Otukpo Ruben Bako, ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na AP ranar Alhamis cewa an kai harin ne ranar Laraba a kauyen Umogidi inda aka kashe mutum 47.

Ya kara da cewa an yi wa mutum uku yankan rago a kauyen ranar Talata. Kakakin ‘yan sandan Binuwai Anene Sewuese ta tabbatar da kai harin tana mai cewa maharan sun bude wuta ne a wata kasuwar kauye.

Sai dai Sewuese ta ce mutum takwas ne suka mutu, ciki har da wani dan sanda.

Har yanzu ba a san dalilin kai harin ba, ko da yake hukumomi sun ce hare-haren biyu suna da alaka da juna.

Ana zargin makiya

Ko da yake babu wanda ya dauki alhakin kai harin, amma hukumomi suna zargin makiyaya da hannu wurin kai shi.

A baya an sha yin arangama tsakanin manoma da makiyaya a jihar ta Binuwai. Manoman suna zargin makiyayan da tura dabbobi cikin gonakinsu inda suke yi musu barna.

Sai dai makiyayan sun sha musamman zargin suna masu cewa burtali kawai suke bi suna kiwonsu kamar yadda doka ta tanada.

Hukumomi sun sha cewa suna daukar mataki domin shawo kan wannan matsala amma har yanzu lamarin ya ci tura.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here