Yan Boko Haram 974 sun mika wuya a Najeriya

0
94

Rundunar Tsaro ta Nijeriya ta ce ‘yan Boko Haram 974 ne suka mika wuya ga sojoji a wurare daban-daban a jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar, bayan wasu samame da dakaru suka yi.

A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ranar Alhamis, Daraktan yada labarai na Rundunar Tsaron Manjo Janar Musa Danmadami, ya ce a makonni biyun da suka gabata dakarunsu sun kai farmakai a yankuna da dama kuma ana samun nasara.

Danmadami ya kara da cewa ‘masu tayar da kayar baya 974 da suka hada da maza manya 77, da mata 364 da kuma yara 533 ne suka mika wuya ga jami’an tsaro a yankunan da aka kai farmakan.

Ya kuma kara da cewa a yayin farmakan an kassara ‘yan ta’addar Boko Haram 21, sannan an kwace kudi da yawan su ya kai naira miliyan 2.3 da wayoyi da kuma manayan makamai irin su gurneti da bindigogi da jigidar harsasai da kayan hada bam da sauran su.

A shekarun 2000 ne kungiyar ta’adda ta Boko Haram ta fara bulla, kuma tun daga 2009 zuwa yau ta kashe sama da mutane dubu ashirin a hare-haren da ta kai.

Daga shekarar 2015 zuwa yau kungiyar ta’adda ta Boko Haram ta kai hare-hare a kasashen Nijar, Chadi da Kamaru da ke makotaka da Nijeriya inda ta yi ajalin a kalla mutane dubu biyu.

Sakamakon hare-haren ta’addancin kungiyar, dubunnan daruruwan mutane sun rasa matsugunansu.

Sauran sassan Nijeriya

Baya ga nasarar da rundunar tsaron ta yi a arewa maso gabashin Nijeriya, sanarwar ta ce rundunar ta kama wasu manyan masu laifi da ake hada kai da su wajen kitsa munanan ayyuka a jihohin Taraba da Binuwai.

Kazalika rundunar ta kai samame maboyar wasu masu satar mutane don kudin fansa a dajin Nimbia da ke karamar hukumar Riyon ta jihar Filato da kuma a jihar Kogi inda ta kama masu satar mutane ta kuma kubutar da wasu fararen hula.

A yankin arewa maso yammacin Nijeriya kuwa rundunar ta yi samamen ne a jihohin Kaduna da Zamfara da Kebbi da Katsina da kuma Sokoto inda ta ceto wadanda aka sace da dama bayan musayar wuta tsakanin dakaru da masu satar mutanen.

A can kudancin Nijeriya kuwa sojojin sun ce sun yi nasara a yaki da masu satar man fetur dafasa bututan mai da sauran miyagun laifuka a jihohin Delta da ayewlsa da Ribas da Cross River a kudu maso kudu.

A kudu maso gabas kuwa nasarar rundunar a kan masu fafutukar kafa kasar Biafra ne inda ta kwace manyan makamai tare da tserar da wasu mutane da ‘yan kungiyar suka kama.

A dukkan samamen nan an kama manya-manyan makamai kamar yadda sanarwar ta fada.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here