Babu daukar fansa a gwamnatin Abba Gida-gida – Hon Bashir

0
131

Shugaban kungiyar hada manufar Abba Gida-gida ta ‘AKY Brother Hood Campaign’, Hon Bashir Abubakar ya bayyana babu daukar fansa a cikin gwamnatin Abba Kabir Yusu (Abba Gida-gida).

Ya ce duk da irin kalubale da suke fuskanta daga gwamnatin mai marin gado, amma hakan ba zai sa a dauki fansa daga wadannan abubuwa ba.

Har ila yau, Hon Bashir ya ce gwamnatin jam’iyyar NNPP ta zo ne da niyar gyara ba daukar fansa ba, babu wata manufa na musguna wa wani a wannan gwamnatin mai jiran gado.

Ya ce babban burin wannan gwamnati ta kawo wa Jihar Kano ci gaba ta kowace fuska da ya shafi bunkasa rayuwar mata da matasa ta hanyar samar da kamarantu masu inganci domin samun ilimi da samar da ayyuka da sana’o’i da sauran al’amuran da suka shafi lafiya da tsaro.

A karshe, Bashir ya kara da cewa babban abun da wannan gwamnati ta Abba Gida-gida take bukata shi ne, addu’a da hadin kan al’uma ta hanyar shawarwari masu inganci da kuma hakuri da ayyukan gwamnati, musammam shi Abba wanda mutum ne da ya zauna da Madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya kuma san tsarin aiki irin na wannan tafiya ta neman mai da Kano lamba daya ta kowace fuska.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here