Buhari ya nemi a kawo ƙarshen tashin hankalin Binuwai

0
86

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da kashe-kashen baya-bayan nan da aka samu a jihar Benue da ke arewa ta tsakiyar ƙasar.

Rahotonni sun ce an kashe gwamman mutane a ƙauyen Umogidi da ke ƙaramar hukumar Otukpo

A wata sanarawa da mai magana da yawun shugaban Malam Garba Shehu ya fitar, Buhari ya ce za a yi duk mai yiyuwa wajen kawo ƙarhen tashe-tashen hankula a ƙasar.

Shugaban ƙasar ya yi Allah-wadai kan amfani da abin da ya kira ta’addanci wajen rura wutar faɗan ƙabilanci a ƙasar,.

Ya kuma bayar da umarnin zaƙulo maharan domin fuskantar hukunci kan laifin da suka aikata.

Shugaban ya kuma jajanta wa iyalan waɗanda suka rasa rayukansu sakamakon harin.

“Muna miƙa sakon ta’aziyyarmu ga iyalan waɗanda aka kashe. Kuma ƙasarmu za ta tsaya tsayin-daka domin yaƙar ayyukan ɓata-gari da na ‘yan ta’adda”, in ji Buhari.

Daga ƙarshe shugaban ya umarci jami’an tsaron ƙasar da su ƙara sanya idanu tare da sake nazarin fannin tsaro musamman a yankunan da lamarin ya faru.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here