Cinikayyar yan wasa: AC Milan zata saki Ibrahimovic, Mpabbe zai zauna a PSG

0
116

Paris St-Germain ta yi wa Real Madrid kancal a burinta na daukar Kylian Mbappe a bazara, inda ta gaya mata cewa ba za ta sayar da dan gaban na Faransa ba kafin 2024.

Haka kuma PSG din za ta sake yunkurin neman dan wasan gaba na gefe na Chelsea Hakim Ziyech, na Morocco a bazara. (Football Insider)

Chelsea za ta duba yuwuwar zawarcin Carlo Ancelotti a karo na biyu idan kociyan ya kammala aikinsa da Real Madrid a karshen kaka. (ESPN)

Wakilin Sofyan Amrabat ya ce Fiorentina za ta saurari tayi daga masu sha’awar sayensa a bazara kuma tuni Manchester United ta gabatar da bukatarta ta sayen dan Moroccon a watan Janairu. (Sport).

An sanya sunan tsohon kociyan Manchester United Ole Gunnar Solskjaer a jerin wadanda za a iya zaba domin cike gurbin da Scott Parker ya bari na mai horad da kungiyar Club Bruges ta Belgium. (Times)

Paris St-Germain ta kara dagewa domin ganin ta sayi matashin dan wasan Ingila Jude Bellingham, mai shekara 19, daga Borussia Dortmund a bazara. (SER Deportivos)

Aaron Ramsey ya yi wasannin da yawansu ya kai kungiyarsa Nice ta kara masa shekara daya a kwantiraginsa, to amma kuma shi da kungiyar na tattaunawa a kan ba shi kwantiragi mai tsawo. (L’Equipe – in French)

AC Milan ba za ta bai wa Zlatan Ibrahimovic mai shekara 41 sabon kwantiragi ba. (FootMercato)

Aston Villa na tattaunawa da dan wasan Ingila Ollie Watkins a kan sabon kwantiragi sakamakon kwazon da yake nunawa a yanzu. (Mail)

Kociyan Feyenoord Arne Slot na cikin wadanda ake ganin za su iya samun aikin kociyan Tottenham a bazara wata biyu bayan da ya ki karbar aikin horad da Leeds. (Express)

Tsohon kociyan Ingila Sam Allardyce zai iya kasancewa mai horad da Leicester City. (Football Insider)

Tsohon kociyan Leeds Jesse Marsch ya tattauna da Leicester a kan aikin horad da kungiyar. (The Athletic)

Newcastle United na sha’awar sayen Youri Tielemans, idan kwantiragin dan wasan tsakiyar na Belgium ya kare da Leicester a bazara. (Football Insider)

Marcelo Bielsa, wanda Jesse Marsh ya gada a Leeds, ya amince ya zama sabon kociyan Uruguay. (TyC Sports)

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here