Home Labarai Yadda Najeriya za ta tsira daga kangin bashin da ya dabaibaye ta

Yadda Najeriya za ta tsira daga kangin bashin da ya dabaibaye ta

0
101

Masu sharhi da masana tattalin arziki a Nijeriya na nuna fargaba kan yadda bashin da ake bin kasar ke karuwa da kuma damuwa kan yadda kusan dukkan kudin da take samu a cikin gida ke tafiya wajen biyan kudin ruwa na bashin.

A ‘yan kwanakin nan Ofishin Kula da Basussuka na Nijeriya DMO ya alakanta dumbin bashin da ake bin kasar da yawan gibin da ake samu a kasafin kudi, da rashin samar da kudaden shiga da yawan bashin da ake ciyowa da sauran su.

Bashin da ake bin Nijeriya ya karu daga naira tiriliyan 39.56 (dala biliyan 95.77) zuwa naira tiriliyan 46.25 (dala biliyan 103.11) a karshen watan Disambar shekarar 2022.

Wata sanarwar da DMO ya fitar a karshen watan Maris ta ce basussukan sun hada da wadanda da ake bin jihohin kasar 36. Naira tiriliyan 27.55 (dala biliyan 61.42) ne bashin da ake bin kasar a cikin gida.

Basussukan da ake bin kasar a ketare kuwa sun kai naira tiriliyan 18.70 (dala biliyan 41.69), in ji sanarwar ofishin.

“Aron kudi da gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohin kasar ke yi don cike gibin kasafin kudi ko kuma yin wasu ayyuka na musamman, na cikin ababen da suka sa bashi ke kara yawa kan kasar, a cewar sanarwar.

Ba da takardar lamuni da gwamnatin tarayyar kasar ke yi na cikin ababen da ke kara yawan bashin kasar, in ji ofishin.

Yawan bashi

Ministar kudin Nijeriya, Zainab Ahmed ta tabbatar da wannan maganar yayin da ta ce kasar ta kashe naira tiriliyan 5.24 kan kudin ruwa cikin naira tirilyan 6.5 da ta samu tsakanin watan Janairu zuwa Nuwaban shekarar 2022.

Ministar ta yi wannan maganar ne a watan Janairun shekarar nan, a lokacin da take bayani a kan kasafin kudin shekarar 2023 da aka amince da shi.

Wannan ya nuna cewar kashi 80.6 cikin 100 na kudin da take samu yana tafiya ne a kan biyan kudin ruwa na bashi. Hakan ya sa wasu ke fargabar cewa nauyin bashin ka iya durkusar da kasar.

Arunma Oteh, wadda ta taba shugabancin kasuwar hada-har hannun-jari ta Nijeria (Nigerian Stock Exchnage) ta ce kasar ba za ta iya kai labari ba idan ta ci gaba da kashe dukkan kudin da take samu a kan biyan kudin ruwa na bashi.

Sai dai kuma ba kowa ne yake da wannan ra’ayin ba. Wasu na ganin cewa akwai mafita ga kasar.

Ofishin DMO ya ce bashin da ake bin Nijeriya bai wuce kashi 22.74 na ma’aunin tattalin arzikin kasar (GDP) ba, yawan da bai kai iyakar da kasar ta saka wa kanta na kashi 40 cikin 100 ba.

Ofishin ya kara da cewa Bankin Duniya da Asusun ba da Lamuni na Duniya IMF sun bayar da shawarar cewa bai kamata kasashe su karbi bashin da ya zarta kashi 55 cikin 100 na ma’aunin tattalin arzikinsu (GDP) ba.

“Idan aka yi la’akari da ma’aunin tattalin arzikin kasa (GDP) da yawan bashin, bashin da ake bin Nijeriya bai kai ya durkusar da ita ba,” kamar yadda Idakolo Gabriel Gbolade, shugaban kamfanin zuba jari na SD&D da ke Nijeriya ya shaida wa TRT Afrika.

“Amma muhimmin kalubalen shi ne idan ba a kara kudin shiga da ake samu daga cikin gida daga shekarar 2023 zuwa 2025 ba, za a iya shiga wani yanayi na tashin hankali a fagen tattalin arziki, wanda zai iya shafar iya ci gaba da biyan kudin ruwa kan bashinmu,” in ji Idakolo.

Masanin tattalin arzikin ya ci gaba da cewa “Wata babbar matsalar kuma ita ce, idan aka samu babban kalubale kan kudin da muke samu ta hanyar man fetur, zai iya tasiri kan iya cigaba da biyan kudin ruwa a kan bashinmu”.

“Abu mai kyau ne cewar danyen man da muke hakowa yanzu ya kai ganga miliyan 1.3 a kowace rana. Sai dai babbar matsalar ita ce a samu mu sayar da man a kasuwar duniya inda ake samun tsaiko wajen sayar da shi,” in ji Idokolo.

Mafita

A wani jawabi da ta taba yi kan bashin Nijeriya a watan Janirun wannan shekarar, Arunma Oteh ta ce ‘yan kasuwan kasar za su iya neman mata mafita idan wutar lantarki ta dore a kasar.

Shi kuwa Idokolo gani yake mafita ga kasar ita ce a cire tallafin man fetur domin gwamnati ta samu kudaden gudanar da ayyuka.

Ya ce cire tallafi na cikin hanyoyin da Nijeriya za ta yi don cire kanta daga kangin bashi.

Tuni gwamnatin Nijeriya ta sanar da cewa daga watan Yunin 2023 za ta daina biyan kudaden tallafin man fetur, lamarin da ke nufin za ta samu rara sosai amma ‘yan kasa kuma za su saye shi da tsada.

Sai dai masana tattalin arzikin sun ce gwmnati na bukatar hanyoyin da za ta bi wajen rage wa mutane radadin cire tallafin man.

Mista Idakolo ya ce ya kamata gwamnatin kasar ta gyara matatun man kasar domin idan dukkan matatun suna aiki yadda ya kamata, zai rage yawan kudin fetur a kasar.

“Bayan tabbatar da cewar gwamnati ta saka kudi sosai a harkar sufuri, ya kamata gwamnatocin kasar su saka kudi kan harkar jirgin kasa ta yadda mutane za su iya tafiya cikin kasar ba tare da sun kashe kudi mai yawa ba,” ya ce.

Ofishin kula da bashin Nijeriya ya ce kokarin da gwamantin ke yi na kara fadada hanyoyin samun kudi ta hanyar mai da kuma wasu hanyoyi da ba na mai ba zai iya sa kasar tsira daga kangin bashi.

Kudin Bankin Duniya

A ranar Larabar da ta gabata ma Ministar Kudin kasar Zainab Ahmed ta ce Nijeriya ta samu kudi dala miliyan 800 daga Bankin Duniya don yin amfani da su wajen rage wa mutane radadin cire kudin tallafin man fetur.

Wannan ya sa wasu suka fara sukar gwamnatin cewa tana aron kudin ne domin ci ba domin ta bunkasa masana’antu ba.

Sai dai Idokolo na ganin kudin da Nijeriyar ta samu daga Bankin Duniya ka iya zama alheri idan kudin ya kai ga mabukata a kasar, don zai hana cire tallafin girgiza tattalin arzikin kasar.

‘Yan Nijeriya na fatan cewa kasar za ta samu ci gaba nan ba da jimawa ta yadda tattalin arzikinta zai bunkasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

X whatsapp