An sake kama mutumin da yake yi wa mata fyaɗe ta hanyar amfani da Facebook

0
158

Gwamnatin Afirka ta Kudu ta ce an yi nasarar sake kamo wani mutum da ya yi ƙaurin suna wajen aikata fyaɗe da kisa wanda ya tsere daga gidan yari bayan ya yi ƙaryar ya mutu.

Jami’ai sun ce an kama Thabo Bester tare da budurwarsa da wani mutum a ranar Juma’a a Tanzania.

An yi wa Bester laƙabi da mai fyaden Facebook saboda yadda yake amfani da shafukan sada zumunta wajen ɗana wa mutanen da yake yaudara tarko.

An yi tunanin ya mutu a wata gobara da ta tashi a gidan yarin cikin shekarar da ta gabata amma gwaje-gwajen da aka yi sun tabbatar da cewa gawar da aka gani, ba ta shi bace.

Lamarin dai ya janyo ce-ce-ku-ce a Afirka ta Kudu – ƙasar da aka fi samun yawan laifukan cin zarafi ta hanyar lalata a duniya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here